19 Mayu 2025 - 15:01
Source: ABNA24
Isra'ila Na Ci Gaba Da Ruwan Bama-Bamai A Khan Yunus

Isra'ila ta kai hari kan Khan Yunis ne domin kashe daya daga cikin manyan kwamandojin Nasser Salahaddin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Da safiyar yau ne sojojin Isra'ila suka kai hare-hare ta sama sama da 30 a kan birnin Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.

Bayan harin an tabbatar da shahadar "Ahmad Kamel Sarhan" babban kwamandan rundunar Salahddin.

Dakarun Nasser Salahaddinl a hukumance sun sanar da shahadar Ahmed Kamel Sarhan, shugaban gudanarwa na musamman na rundunar da dakarun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi. Haka tashar yada labarai na Al-Mayadeen ya bayar da rahoton cewa, an shahadantar da Ahmed Kamel Sarhan a wani hari da dakarun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a Khan Yunus.

Bayan nan kuma Hukumomin mamaya sun ba da umarnin ficewa daga garin Khan Yunis nan take a shirye-shiryen kai hare-haren da ba a taba gani ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha